Cote d’ivoire

Fira Ministan Kenya Yace Sasanta Rikicin Cote d'ivoire Ya Faskara

Fira Minista Raila Odinga na ban kwana da Laurent Gbagbo
Fira Minista Raila Odinga na ban kwana da Laurent Gbagbo rfi

Fira Ministan  kasar Kenya Raila Odinga wanda yake ta safa-da-marwa zuwa kasar Cote D’Ivoire domin sasanta rikicin siyasar kasar, yace lokaci na kara kurewa Laurent Gbagbo daya sauka ya mika mulki ga wanda ya lashe zaben Shugabancin kasar Alassane Ouattara.Da yake Magana da manema labarai da saukan sa a Nairobi, Kenya daga Cote D’Ivoire, Raila Odinga yace yayi iyakacin kokari amma  Laurent Gbagbo yayi kememe.Odinga yace sunata wannan hakilo ne domin gudun kada a zubar da jinni a wannan kasa inda rayukan mutane 260 ya zuwa yanzu suka salwanta.Karshen wannan wata ne ake saran Kungiyar kasashen Afrika zasu dauki mataki na karshe gameda kafewar da Laurent Gbagbo yayi bisa madafun iko na kasar.