Davos-Switzerland
An Fara Taron Tattalin Arziki Na Duniya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, Jacques Diouf, yace za’a cigaba da samun zanga zanga a kasashen duniya, sakamakon tsadar abinci.Yayin da yake jawabi wajen taron tattalin arziki a Davos, na kasar Switzerland, Diouf ya bayyana cewar.lalle idan an cigaba da samun hauhawan farashin kayan abinci, musamman idan ba a samu kyakyawar girbi ba, a damuna mai zuwa, lalle za’a fuskanci mawuyacin hali.