Amirka

Republican Sun Kushe Obama

Shugaba Barack Obama.
Shugaba Barack Obama. rfi

Jamiyyar Republican ta zargi shugaba Barack Obama, da Gwamnatin Democrat da gazawa wajen tafi da kasar, wajen haifar da gibin kasafin kudi, da kuma kashe kudaden da basu dace ba.Yayin da yake maida martani bayan jawabin shugaba Obama ga Majalisar kasar, Dan Majalisa Paul Ryan, ya bayyana cewar.Shugaban kasa da Jam’iyar democrat sun bayyana ta aiyukansu cewar, ya dace Gwamnati ta kara yawan jami’an ta da kuma aiyukan ta, kimar ta da kuma karfin ta, ta hanyar bada tallafi ko zuba jari, kudirin ta ya nuna cewar, suna bukatar Gwamnati dake mamaye komai, kara yawan haraji, da kuma kashe kudi da yawa, a cikin shekaru biyun da suka gabata abinda muka gani kenan, mu muna da shirin cigaba da ya zarce wannan.