france

Shugaba Sarkozy na hallartar taron kungiyar tarrayar Afrika

Nicolas Sarkozy da  Ban Ki Moon na ganawa a wurin taro
Nicolas Sarkozy da Ban Ki Moon na ganawa a wurin taro Reuters

A yau ne ake bude taron kungiyar tarrayar Afrika karo na 16 a garin Addis- Abeba babban birnin kasar Habasha.Rikicin kasar Cote-D’Ivoire na daya daga cikin mahimman abubuwan da za a tautaunawa.Taron zai samu hallartar Nicolas Sarkozy,shugaban kasar Franshi wanda tuni ya samu isa a garin na Habasha a sahiyar yau.A na kallon kasar Franshi a matsayin kasar da ke da ruwa da tsaki a cikin maganar rikicin kasar Cote- D’Ivoire. A wurin taron shugaban Sarkozy zai yi bayani a game da dangantakar hulda tsakanin kasashen Afrika da na duniya a daidai wanan lokaci da kasar Franshi ke jagorentar kungiyar kasashe 8 da kuma ta kasashe 20 mafi karfin tatatlin arziki da masu karfin fada a ji a duniya,wato G8 da G-20.