Libya-France

France da Britaniya sun kira taro kan Libiya

François Fillon da David Cameron
François Fillon da David Cameron REUTERS/Peter Macdiarmid/Pool

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, tare da Praministan Britaniya, David Cameroun, sun yi kiran taro na musamman dan sake daukar mataki kan kasar Libya.A tattaunawar da su ka yi ta wayar tarho, shugabanin biyu sun amince da baiwa masanan kasahensu damar bada shawara kan matakan da ya kamata a dauka, dan kawo karshen rasa rayuka a Libya.