France-Libya

Faransa Tayi Gargadi Game Da Tura Dakarun NATO Zuwa Libya

Ministan Waje na kasar Faransa Alain Juppe
Ministan Waje na kasar Faransa Alain Juppe rfi

Kasar Faransa tayi gargadi kan duk wani shiri na tura dakarun kungiyar Tsaro ta NATO kasar Libya, inda tace hakan zai zama wani koma baya, a idan kasashen larabawa.Ministan harkokin wajen kasar, Alain Juppe ya bayyana haka, inda yake cewa, daukar matakin bazai samu karbuwa ba.Shima Sakataren Tsaron Amurka, Robert Gates, yace ya zuwa yanzu, babu wata yarjejeniyar anfani da karfi wajen kifar da Gwamnatin shugaba Muammar Ghadafi.