Libya-EU

Gaddafi Ya Sake Yiwa Mutan Kasar Jawabi

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya bukaci Shugaban kasar Libya Moamer Kadhafi daya amince ya sauka daga karagar mulkin kasar.Manuel Barroso yace yau laraba ya dace Moamer Kadhafi ya ajiye aikin nasa.

Shugaban kasar Libya Moamer Kadhari
Shugaban kasar Libya Moamer Kadhari rfi
Talla

KUNGIYAR KASASHEN TURAI EU ZASU YI TARO GAMEDA LIBYA

Yace irin yadda Hukumomin kasar Libya suka rika yadda suke so cikin makon daya gabata babu dadi kuma ba abin amincewa dashi bane.

Barroso wanda yake jagorantar Hukumar kasashen Turai 27 dake cikin kungiyar su, yace abin bukata shine Kadhafi ya sauka kamar yadda mutan kasar suke bukata.

A wani labarin Shugaba Moamer Kadhafi cikin jawabinsa karo na uku yau laraba ya zargi kungiyar Al-Qaeda da alhakin zanga zangan da akeyi masa a kasar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI