France-South Africa

Zuma Ya Fara Rangadi A Faransa

Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma
Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma rfi

Shugaban  Kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, ya fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Faransa, inda ake saran yau zai gana da shugaba Nicolas Sarkozy.Wannan ziyara na daga cikin  yunkurin sa na kawo sauyi kan harkokin kasuwanci, a karkashin shugabancin kungiyar kasashe 20 da suka fi habakar tattalin arziki a duniya.