Muhallinka Rayuwarka

Kiwon Kifi

Sauti

Ko da yake Kiwon kifi bai zama ruwan dare kamar kiwon dabbobi na cikin gida ba, mutane kadan kadan sun soma gane kiwonsa ko in ce nomansa a cikin gidajensu ko a cikin tabkuna (taukuna). inda ana iya lissafta kiwonsa na daya daga cikin matakan yaki da talauci gadan gadan saboda sauki. A Jamhuriyar Niger akwai Masunta da masu sana'ar kifi da yawa masu son harakar kion kifi amma karfinsu ya kasa; a cikin wannan shirin sun mika kuka ga hukumomi da kungiyoyi masu hannu da shuni na su taimaka masu a cikin gurinsu na yaki da talauci albarkacin kiwon kifi.