Cote d’ivoire

Manyan Gidajen Radio Basa Aiki A Cote d'Ivoire

Mutane na ta barin wuraren da ake fargaban rikici a kasar Cote d'Ivoire
Mutane na ta barin wuraren da ake fargaban rikici a kasar Cote d'Ivoire rfi

RAHOTANNI Daga kasar Cote d’Ivoire, sun nuna cewa, an daina jin sautin Radio Faransa da BBC jiya, kwana guda bayan dakatar da aiyukan kanfanonin wasu Jaridu masu zaman kansu.Wakilin Radio Faransa a Abidjan, Marco Oved, yace da rana ne aka daina jin sautin tashoshin, kuma ana zargin magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo kan lamarin.