Libya

Sojan Libya Na Ta Luguden Wuta Kan Masu Zanga Zanga

Sojan sama na kasar Libya na ta ruwan harsasai kan masu zanga zangan lumana dake neman Shugaba Moamer Gaddafi daya sauka daga mulkin kasar.Luguden wutan na yau yafi kamari ne a garin Brega inda aka sami mutane akalla 12 da suka mutu jiya a gwabzawa da akayi tsakanin bangarori biyu na masu goyon bayan zanga zangan da  wadan da basa son ra’ayin A wani labari Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da abinci ta bada gudumawan dala milyan 38.7, na gaggawa domin tallafa wa mutane kusan milyan uku da rikicin kasar Libya ya ritsa dasu.Dr Badayi Sani masanin tattalin arziki ya shaida mana mahimmacin haka: 

Wani mutun ya rufe kunnuwan sa lokacin da aka saki bam a garin Brega
Wani mutun ya rufe kunnuwan sa lokacin da aka saki bam a garin Brega rfi
Talla

Bakin ‘yan kasashen ketere na ci gaba da kokawa kan halin da suka samu kansu na rikicin kasar Libya, inda ‘yan kasashe musamman na Afrika ke neman gwamnatoci sukai musu dauki.

Hussaini Halla Dan Janhuriyar Niger ya nemi taimakon mahukunta domin mayar dasu gida:

Halin Da 'Yan Kasashen Waje Suke Ciki A LIBYA

A halin da ake ciki kasar Faransa ta tura jirgin ruwan yakin ta, na biyu wajen girma, mai daukar jiragen saman yaki masu saukar ungulu, zuwa mashigin ruwan Libya, dan kwashe Yan kasar Masar da suka makale akan iyaka.

Ma’aikatar tsaron tace, jirgin zai gudanar da aiyukan agaji ne, a karkashin kungiyar kasashen Turai, yayin da shugaba Muammar Ghadafi ke cewa, babu abinda zai sashi sauka daga karagar mulki.
Ga dai abinda yake cewa.
 

akwai shirin kai dakarun kasashen waje, amma munafincin ya fito fili, kuma babu yadda zasu mamaye man fetur din mu, wanan ba zai yiwu ba, ba zai yiwu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI