Libiya

Ana Cigaba Da Barin Wuta A Libiya

Mayakan dake fafatawa a yankin Brega na Libiya
Mayakan dake fafatawa a yankin Brega na Libiya rfi

Sojan kasar Libya dake goyon bayan Shugaban kasar Moamer Gaddafi sun cigaba da barin wutan kan wadan da suke zanga zangan nuna kyamar Gwamnati a yankin Az Zawiyah kusa da birnin Tripoli.Bangaren ‘yan adawan kasar sunma suna mayar da martani da harsasai.Aya zuwa yau Asabar Dakarun kasar Libyan sunyi katarin sake kwace wasu garuruwan da suka subuce masu.Wasu bayanai na cewa mutane akalla 30 suka rasa rayukan su sakamakon barin wuta da akayi tayi.Dubban masu bore ya zuwa dazun nan nata kara taruwa a filin da suke zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin.