Tunisiya

An Rusa Yan Sandan ciki na Tunisiya

Prime Ministan Tunisiya Béji Caïd Essebsi
Prime Ministan Tunisiya Béji Caïd Essebsi AFP/FETHI BELAID

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunisiya, ta sanar da rusa rundunar 'yan sandan ciki, ta kasar, wanda aka zarga da cin zarafin jama’a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Zine el-Abidine Ben Ali.Prime Ministan kasar, Caid Essebsi, ya bayyana haka, tare da sanar da wata sabuwar gwamnati, wanda bata kunshi jami’an tsohuwar gwamnatin Ben Ali da ba, wanda boyen mutane ya kawo karshen gwamnatinsa ta shekaru 23.Juyin juya halin kasar ta Tunisiya ya yi tasiri cikin daukacin kasashen Larabawa, inda yanzu ake fama da masu zanga zangar neman kawo sauye sauye na demokaradiya tare da neman ganin bayan mulkin kama karya.