Libiya

Takunkomi na reto a wuyen Libiya game da zirga-zirgar jirage.

Kanal Kadhafi  na nuna samun nassara
Kanal Kadhafi na nuna samun nassara REUTERS/Ahmed Jadallah

A wata hira da tashar talabijin ta kasar Turkiya, shugaba Muammar Ghadafi ya ce mutanen kasar ba za su amince ba da duk wani yunkuri na hana shawagin jiragen sama .A yanzu haka, kasashen Yammacin duniya na nemna ganin an kakabama kasar takunkumi.Shugaban ya ce, mutanen kasar a shirye suke su dauki makamai dan kare kansu daga dukkan wata barazana.Rahotanni sun ce, Kasashen Faransa, Britaniya da Amurka, sun kamala tsara daftarin da kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai amince da shi, akan kasar ta Libya.Kungiyar kasashen Turai ta hannun babar jami’ar diplomasiyar ta, Catherine Ashton, ta bukaci shugabanin kasashen duniya da su daina hulda da shugaba Ghadafi.Majalisar tafiyar da mulki a kasar ta Libya, da Yan Tawaye suka kafa, taki amincewa da duk wata bukata ta tura sojin kasashen waje kasar ta Libya.