Dakarun Gaddafi Na Kara Kutsawa Sansanonin "Yan Tawaye
Dakarun dake goyon bayan Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi na ta kara kai hare hare kan masu zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin kasar dake gabashin Benghazi.Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Kimoon ya bukaci a tsagaita wuta cikin gaggawa.Yayin da rikicin ke kara kazancewa da samun hasarar rayuka da yawa, Sakatariyar Waje na kasar Amirka Hillary Clinton na fatan Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya zatayi wani abu cikin gaggawa domin shawo kan rikicin.A halin da ake ciki Kasar Amirka ta gargadi Hukumomin kasar Libya da kada su kuskura su tsare manema labarai dake aiki.Gargadin na biyo bayan bacewar wasu ‘yan jaridun kasar Amirka hudu ne da suka bace a kasar Libya.
Wallafawa ranar: