Cote d’Ivoire
An Kashe Mutane 4 A Cote d'Ivoire
Mutane hudu ne aka kashe a kasar Cote d’Ivoire a gwabzawa tsakanin magoya bayan Shugaba Laurent Gbagbo da kuma zababben Shugaban kasa Alassane Outtara.Wani shaidan gani da ido ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa y aga mutane uku dauke da bindiga mai sarrafa kanta, inda suka fita daga motar taxi, kum suka bude wuta kan mai uwa da wabi.Fatou Bensouda, itace mataimakiyar mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka, kuma kamar yadda take cewa rikicin kasar Cote d’Ivoire ya kama hanyar zama yakin basasa, fatar da ake yi shine kada lamarin ya tabarbare.
Wallafawa ranar: