Niger

Seini Oumarou Ya Amince Da sakamakon Zabe

Seyni Oumarou
Seyni Oumarou rfi

Tsohon Fira Ministan kasar Janhuriyar Nijar kuma dan takaran Shugabancin kasar daya sha kaye a zagaye na biyu na zaben Shugabancin kasar Seini Oumarou ya amince da sakamakon zaben na ranar Asabar data gabata.Mahamadou Issoufou tsohon dan hamayya shine yayi nasaran lashe zaben Shugabancin kasar.Seini Oumarou ya shaidawa magoya bayan sa a birnin Niamey cewa ya karbi sakamakon zaben da Hukumar zaben kasar, CENI, ta bayar cewa ba shine yayi nasaran zaben ba.Yayi amfani da daman inda ya taya sabon Shugaban kasar, Mahamadou Issoufou murnar lashe zaben.