Bahrain

"Yan Sandan Bahrain Na Farautar Masu Bore

Dakarun Bahrain da suka karbe filin Pearl Square
Dakarun Bahrain da suka karbe filin Pearl Square rfi

Daruruwan "Yan Sanda a kasar Bahrain, sun yi nasarar kwace Dandanlin Pearl, dake birnin Manama, daga hannun masu zanga zanga, wadanda ke neman shugaban kasar, ya sauka daga karagar mulki.Matakin na zuwa ne kwana guda, bayan Sarki Hamad, ya karfafa matakan tsaro, da taimakon sojin Saudi Arabia da kasar Daular Larabawa.Rahotanni sun ce, an ji karar bindiga, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu ke cigaba da shawagi a birnin.