Libya-France

An Fara Barin Wuta A Libya

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy, wanda yake karban bakuncin baki dake taro gameda kasar Libya,yau Asabar a birnin Paris, ya nuna cewa Shugaba Moammar Gaddafi na Libya  ya janyowa kansa reshe, kuma ya boni.Sarkozy na magana ne bayan taron musamman gameda kasar Libyan da akayi dazun nan a  Paris, daya kunshi wakilan kasar Amirka,Kungiyar kasashen Turai da kuma kasashen Larabawa.Shugaban Faransa  yace mahalarta taron sun amince da ayi amfani da karfi soja,  don tilastawa  Gaddafi  biyayya ga sharuddan  Majalisar Dinkin Duniya.Jiragen yakin kasar Faransa masu tarin yawa sunyi ta shawagi sararin samaniyar kasar Libya yau, ashirin da akeyi domin tsaurara aiwatar da kudirin  Majalisar Dinkin Duniya  dake hana Hukumomin kasar Libya uzurawa masu bore. Bayanai dake shigo mana na cewa jiragen yakin Faransan sunyi shawagin a samaniyar  kasar Libya  lami-lafiya ba tare da matsala ba.Wasu rahotanni daga  Libya na cewa dubban mutane nata tserewa daga wurarenda ake ta gwabza fada tsakanin Dakarun kasar da masu zanga-zangan kin jinin Gwamnatin Moammar Gaddafi.Wasu byanan na nuna ana ta jin aman manyan bindigogi a yankin Bengazi, da ake samun yawan masu kyamar Gwamnatin Gaddafin.Hakanan kuma wasu jiragen yaki sunyi ta kai farmaki yankin Bengazin domin har daya daga cikin jiragen ya rikito kasa.Tun wayewar gari yau  hanyoyin motoci suka chunkushe da  jama’a shake  ana ta tserewa zuwa wasu wuraren da za'a fake.  

Mahalarta taron yau a Paris game da kasar Libya
Mahalarta taron yau a Paris game da kasar Libya rfi