Benin

'Yan Adawa Na Kalubalantar Zaben Boni Yayi

Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi.
Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi. rfi

Babban ‘Dan Adawa a zaben Shugabancin kasar Benin da aka gudanar makon jiya, yayi barazanar kalubalantar zaben da akayi wa Shugaba maici Thomas  Boni Yayi.Sakamakon zaben dai na nuna cewa Shugaba Thomas Boni Yayi ya sami kuriu kashi 53% yayinda shi babban dan adawan, Adrien Hongbeji ya sami yawan kuriu 36%.Bangaren ‘yan adawan sun fadi cewa magudi ne tsagwaronsa aka tafka a zaben.