Libya

Ana Ruwan Harsasai A Kasar Libya

Irin barna da akayi wa kasar Libya
Irin barna da akayi wa kasar Libya rfi

Hare Haren da kasashen Yammacin duniya suka gabatar a kaasr Libya, ya rutsa da gidan shugaba Muammar Ghaddafi, wanda kasar Amurka tace nan ne Cibiyar bada umurnin soji.Garba Aliyu Zaria ya hada mana rahoto akai. 

Talla

Kungiyar Kasashen AU Na Son Ayi Sannu Gameda Libya

A halin da ake ciki Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, ta bukaci bangarorin rikicin siyasar kasar Libya, da suyi taka tsan tsan.

Bayan wani taro da sukayi, shugaban kasar Mauritaniya, Mohammed Ould Abdul’aziz, yace sun ki amincewa da anfani da soja dan warware matsalar.

Haj Salamatu Suleiman, Ministan kasa a ma’aikatar harkokin wajen Nigeria, ta bayyana mana matsayin Nigeria kan rikicin.

A yanzu haka Shugaban  Kasar Venezuela, Hugo Chavez, yayi Allah wadai da harin da kasashen Yammacin duniya suka kaddamar kan kasar Libya, inda ya bukaci tattaunawa dan warware rikicin.

Shugaba Chavez wanda ya zargi kasahsen Yammacin duniya, da neman mamaye man fetur din kasar Libya, yace jefa bama bamai cikin Libya, ba zai warware matsalar ba.

Tuni kasahsen Russia da China suka bayyana irin wannan damuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.