Syria
Ana Ta Gwabza Fada A Syria
Wallafawa ranar:
A kasar Syria dubban jamaa ne suka cigaba da zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin kasar a kudancin birnin Daraa.Bayanai na nuna Daraa ne sansanin masu nuna kyamar Gwamnatin kasar, dake zanga zanga tun ranar Jumaa data gabata duk da cewa akwai tarin jamian tsaro da aka watsa su domin sanya kafar wando daya da masu bore.Masu bore dake kwaikwayo abinda ya faru a kasashen Tunisia da Masar na bukatan aiwatar da sauye sauye ne musamman jingine dokar ta baci da aka kafa na shekaru 48 karkashin shugabancin Shugaba Bashar al-Assad da mahaifin sa Hafez.