Yemen

Babban Sojan Kasar Yemen Ya Shiga Masu Bore

Masu zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin Yemen
Masu zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin Yemen rfi

A kasar Yemen manyan sojojin kasar masu yawan gaske ne suka shiga zanga zangan nuna kyamar Gwamnatin kasar karkashin Shugabancin Ali Abdallah Saleh.Gwamnan gari na biyu wajen girma a kasar, Aden yana daga cikin wadanda suka bijirewa Gwamnatin kasar.Bayanai na nuna cewa tankunan yaki sunyi ta sintiri a birnin Sanaa bayan da Babban Kwamandan Soja dake kulada Tankunan yakin kasar Janar Ali Mohsen al-Ahmar ya ajiye mukamin nasa domin shiga masu zanga zangan kyamar Gwamnati.Da yawa daga cikin kananan sojojin kasar sun bi sahun sa.