Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Ana Kara Samun Gawan Mutane Da Suka Fadi A Jirgin Sama

Fasalin irin jirgin kaya da ya fadi
Fasalin irin jirgin kaya da ya fadi rfi

An sami karin wasu gawa hudu daga inda jirgin Sama ya fadi a kasar Janhuriyar Congo, wanda ya kawo jimillan mamata 23 da suka mutu cikin jirgin saman.Jirgin wanda na dakon kaya ne ya rikito cikin gidajen jama’a ne a garin Pointe-Noire.Jirgin saman ya fadi ne lokacin da yake kokarin sauka.Cikin mamatan da aka sami gawansu akwai ‘yan kasar Russia hudu dake aiki da jirgin.