An Sami Baraka A Cigaba Da Kaiwa Libya Hare Hare
Rahotanni sun nuna cewar, an fara samun baraka tsakanin kasashen dake goyan bayan kai hare hare ga kasar Libya, inda kasar Italy da tayi alkawarin bada jiragen ruwan yaki takwas, take cewa, ita bata goyi bayan kaddamar da yaki kan Libya ba, kamar yadda Ministan harkokin wajen kasar, Franco Frattini ya bayyana.Wanann matsayi yayi dai dai da na kasar Jamus, inda Ministan harkokin wajen ta, Guido Westerwelle yace, sun yi nazarin hatsarin dake cikin aikin, kafin suka dauki matsayin rashin amincewa.Fira Ministan kasar Britaniya David Cameron yace ba haka abin yake ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jawabin da Fira Ministan Britania David Cameron yayi
''Wannan shiri ne na kare mutane, da kuma baiwa mutanen Libya dama su tsarawa kansu abinda suke so.''
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu