Libya-France-UN

Shugaba Sarkozy Ya Ziyarci Sansanonin Da Jiragen Yakin Kasar Ke tashi Zuwa Libya

Jiragen yaki dake kai hare hare kasar Libya
Jiragen yaki dake kai hare hare kasar Libya rfi

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya ziyarci tsubirin Corsica inda nan ne zangon kaiwa kasar Libya hare hare ta sama.Ministan tsaro na Faransa Gerard Longuet ne ya rufawa Shugaba Sarkozy baya, kamar yadda maaikatar tsaron kasar Faransa ke cewa.Daga ranar Asabar zuwa yau jiragen yakin kasar Faransa sun kai farmaki kasar Libya sau da yawa domin tilastawa kasar biyayya ga kudurorin majalisdar Dinkin Duniya. A halin da ake ciki, Dakarun kasashen waje dake yaki a kasar Libya na shirinamfani da Sojojin ruwa domin ganin babu wata kasa a fadin duniya data kaiwa kasar Libya daukin makamai.