Muhallinka Rayuwarka

Cike Tekun Lagos

Sauti

Nan da wasu ‘yan shekaru, Biirnin Lagos, cibiyar kasuwanci a tarayyar Nigeria nashirin samun wani sabon kasaitaccen birnin da za a samar da shi ta hanyar cikewani bangaren tekun atlantica. Ana dai sa ran wannan sabuwar anguwar zata kunshi kimanin mutane dubu 250, kumatuni har aiki ya yi nisa kan wanna shirin. Wannan dai shine ake tunanin zai kasance gari mafi kasaita da za a yi a kan fadamar da aka cike.Tuni dai har an fara wannan aikin da ake gudanrwa karkashi wani shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Lagos da wasu kamfanoni masu zaman kansu. Wannan shine abin da za mu duba a cikin shirin na wannan lokacin wanda ni NasiruddeenMohammad zan gabatar.A yi saurare lafiya.