Jamiyyar Shugaba Sarkozy UMP Na Fuskantar Matsala
Wallafawa ranar:
Jamiyyar Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy UMP ta fuskanci matsaloli da dama a zagaye na biyu na kananan zabuka na kananan Hukumomi da aka gudanar ranar lahadi data gabata.Jamiyyar Adawa ta Socialist Party da kuma National Front ne suka sami nasara a zabukan.Jamiyyar Socialist Party ta sami kashi 36 % na kuriu, yayin da Jamiyyar UMP ta sami kashi 20%, sai Jamiyyar National Front ta sami kashi 125 na yawan kuriu.Kasancewar saura watanni 13 a gudanar da zaben Shugaban kasa, Shugaban Jamiyyar Socialist Party Martine Aubry ya fadawa dafifin magoya bayan jamiyyar da suka taru a Hedkwatan Jamiyyar dake Paris cewa sun fara hangen nasaran gaske gaba.