Libya

NATO/OTAN Ta Karbi Karawa Da Libya Har An Kai Hari Mahaifar Shugaba Gaddafi

Wasu 'yan tawaye na murnar nasarar fatattakan sojan Gaddafi
Wasu 'yan tawaye na murnar nasarar fatattakan sojan Gaddafi rfi

Kungiyar kasashen NATO/OTAN ta karbi ragamar tunkaran kasar Libya, daga hannun kasar Amirka, domin hana ta tursasawa fararen hula, kamar dai yadda kudirin  Majalisar Dinkin Duniya ya bukata.Garba Aliyu Zaria ya hada mana rahoto akai. 

Talla

Dakarun NATO/OTAN Sun karbi yakin Libya

A halin da ake ciki kuma, Dakarun kawancen kasashen duniya sun zafafa hare hare ta sama a birnin Sirte mahaifan shugaban Libya Muammar Gaddafi, wanda ya zama birni na gaba da masu adawa suka saka himman kamawa.

Anji fashe fashe a birnin, da kuma Tripoli babban birnin kasar, wuraren da dakarun na Yammacin Duniya ke ci gaba da tabbatar da kudirin Majalisar Dinkin Duniya, wannan bayan kungiyar tsaro ta NATO/OTAN ta karbi ragamar tabbatar da hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar.

Sakataren kungiyar ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya bayyana cewa "kungiyar NATO zata aiwatar da dukkanin sassan kudirin Majalisar babu dadi babu kari".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.