Yanzu haka dai binciken likitoci ya gano yawancin mutanen da suke yanke wa hannu ko kafa kan samo asali ne daga daurin gargajiya maimakon suje asibiti, wanda hakan ka zame musu matsala, daga baya kuma suje asibiti a yanke.Wannan al’amari ya zame wa likitocin wannan fanni matsalar day a haifar musu da rubuce-rubuce, tare da yin kananan taro dan wayarwa da masu dorin gargajiya kai, dan ganin an samun saukin matsalar.Dr Isma’il lawal Dahiru dake bangaren kula da lafiyar kashi yayi Karin bayani a kai.