Libya-OTAN

Halin Da Ake Ciki A Kasar Libya

Jiragin Yakin Faransa dake shirin kai samame Libya
Jiragin Yakin Faransa dake shirin kai samame Libya rfi

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kare matakin tura dakarun kasar zuwa Libya, tare da cewa mataki ne takaitacce.Ya bayyana cewa gobe kungiyar tsaro ta NATO-OTAN zata fara aikin, tare da cewa za'a  nemi sauya gwamnatin kasar ta Libya. Ga abinda Shugaban kasar Amirka Barack Obama ke cewa game da shigan kasar lamarin kasar Libya.

Talla

 

Amirka ta kare shigan ta Lamarin libya

"Manyan abokanmu NATO zata karbi aikin jagorantan tabbatar da hana shawagin jiragen sama na shiga da makamai. NATO ta amince da karin aikin kare fararen hular Libya. Wannan sauyi daga Amurka zuwa NATO za ayi ranar Laraba."

"Ina da karfin gwiwa dakaru zasu saka matsin lamba wa sauran dakarun Gaddafi.
Kungiyoyin dake adawa da gwamnatin kasar Libyasun kara zumma neman kama biranen da suka zama tungar gwamnatin kasar."

Wannan bayan hari dakarun kasashen Yammacin Duniya karkashin kungiyar tsaro ta NATO-OTAN ya gurgunta karfin Shugaba Muammar Gaddafi.

Ibrahim Yahaya mazaunin birnin Gad na kasar ta Libya ya shaida mun halin da ake ciki
 

Halin Da Ake Ciki A Kasar Libya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI