Rikicin Siyasar Cote D'Ivoire Na Munana
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na ganin za'a sami karin ‘yan gudun hijira dake tserewa daga kasar Cote d’Ivoire zuwa kasar Ghana.Melissa Fleming, mai magana da yawun Hukumar ya fadi cewa ya zuwa yanzu akwai ‘yan gudun hijira 3,129 da suka isa kasar Ghana daga birnin Abidjan na Cote d'Ivoire inda kazamin fada ke cigaba.Bayanai na nuna cewa mayaka dake goyon bayan Alassane Outtara da ake ganin shine duniya ta amince dashi nata samun nasara.A halin da ake ciki, ana ci gaba da samun tashe tashen hankula cikin kasar Cote d’Ivoire tsakanin dakarun dake biyayya ga Laurent Gbagbo da ya ki amincewa da shan kaye yayin zabe, da kuma masu biyayya ga Alassane Ouattara da duniya ke dauka zababben shugaban kasa.Ousman Toure mazaunin birnin Abidjan, ya shaida mana yadda haka ke ci gaba da haifar da ‘yan gudun hijira:
Ousmane Toure
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu