Cote d’Ivoire

Dakarun Outtara Na Samun Galaba A Cote d"Ivoire

Mayakan Alassane Outtara na mamaye kasar
Mayakan Alassane Outtara na mamaye kasar rfi

Rahotanni daga kasar Cote d’Ivoire na nuna cewa Dakarun dake goyon bayan Alassane Outtara, wanda duniya ke ganin shine ya lashe zaben kasar, nata mamaye kasar da niyyar fatattakan Laurent Gbagbo wanda yaki sauka daga mulkin.Bayanai na nuna cewa Dakarun Alassane Outtara ya rage masu saura kilomita 200 domin kwace manyan garuruwa biyu dake gaban ruwan kasar.Majalisar Dinkin Duniya tace Dakarun dake goyon bayan Laurent Gbagbo sun bude wuta kan fararen hula inda suka kashe 10 jiya a birnin Abidjan.Bangaren Laurent Gbagbo sun musanta zargin.