Libya

Manyan Kasashen Duniya Na Matsawa Gaddafi Ya Sauka

Mayaka 'yan tawaye dake kasar Libya
Mayaka 'yan tawaye dake kasar Libya rfi

Shugabannnin manyan kasashen duniya da suka yi taro a birnin London kan rikicin kasar Libya, sun fara matsa lamban ganin shugaba Muammar Gaddafi ya yi ban kwana da madafun iko, tare da alwashin ci gaba da kare fararen hula.Shugaban kasar Amurka Barack Obama bai kawar da yuwuwar bada makamai wa ‘yan tawaye ba, domin kawar da Gaddafi. Ana ci gaba da jin kara fashe fashe a birnin Tripoli.Fira Ministan kasar Qatar Hamad Ben Jassem ya nemi sauran kasashen Larabawa su shiga cikin shirin:

Talla

Hamad Ben Jessem

''Abunda muka gani a kwanakin farko, mun ga abun kunya mu zama ‘yan kallo, mu ce ba damuwarmu bane, nayi murya da Larabawa suka shiga da.''

Yanzu haka dai yakin kasar Libya yasa 'yan kasashen Yammacin Afrika cikin mawuyacin hali.

A garin Agadez na kasar Nijar, wanda ke kan iyakan Nijar da kasar Libya na daya daga cikin wuraren da ke cikin wani hali kamar yadda Illa Kane, wani dan jarida ke cewa.

Illa Kane

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.