Cote d’ivoire

Mayakan Outtara Na Kusa da Kama Yamoussoukro

Mayakan Alassane Outtara na mamaye kasar ta Cote d'Ivoire
Mayakan Alassane Outtara na mamaye kasar ta Cote d'Ivoire rfi

Mayakan dake goyon bayan Alassane Outtara da duniya ke ganin shine ya lashe zaben Shugaban kasa a Cote d’Ivoire na gabda yin sauya a babban birnin kasar Yamoussoukro.Bayanai da dimidimi na nuna cewa mayakan sun fatattaki mayakan Laurent Gbagbo, wanda yaki sauka ya mika mulki ga Alassane Outtara.Fararen hula masu yawa na samun mafaka a Choci-choci da wasu wurare domin kare rayukansu.Mayakan Alassane Outtara tun da fari yau sun sami kama garuruwa biyu dake kasar.