Najeriya

Masu zaben Tarayyar Najeriya sun fara jirar sakamakon zabe

Shugaban kasar tarayyar Nigeria Goodluck Jonathan ya yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar jiya Asabar, inda ya ke fuskantar gagarumin kalubale daga tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Muahammadu Buhari mai murabus.Jonatahan yana takara karkashin tutar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, yayin da Janar Muhammadu Buhari ke takara karkashin sabuwar jam'iyyar adawa ta CPC.A shiyar kudu maso gabashin tarayyar ta Nigeria, mazauna yankin sun koka da wasu abubuwa da suka faru yayin zaben shugaban kasa na jiya Asabar, amma dukda haka sun yaba, saboda zaben ya nuna fara smun ci gaba.