Madagascar

Zaben Shugaban Kasar Madagascar Kafin Karshen Shekara- Inji Rajolina

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina
Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina rfi

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajolina yace zai shirya zaben Shugaban kasar kafin karshen wannan shekaran, kuma yana ganin babu shakka shine zai lashe.Wannan matalauciyar kasa dai ta tsunduma cikin rikicin siyasa ne tun lokacin da Shi wannan Shugaba, Andry Rajolina, bara waccan yana magajin gari, da taimakon Sojan kasar ya wanchakalar da Gwamnatin Marc Ravalmanana, ya dare kujeran.Kungiyar kasashen Turai a bara ta dakatar da baiwa kasar tallafi, saboda gaza shawo kan rikicin siyasar kasar.