Spain

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Girgizan Kasa A Spain

Jamian kasar Spain na duba lahanin da girgizan kasa tayi a Lorca
Jamian kasar Spain na duba lahanin da girgizan kasa tayi a Lorca rfi

A kasar Spain mutane a kalla 10 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wata girgizan kasa inda mutane samada 130 suka sami munanan raunuka.Samada shekaru 50 kenan ba'aga irin wannan mummunar girgizan kasa ba data ratsa garin Lorca.Uku daga cikin mamatan mata ne, daya tana da ciki, kamar yadda Magajin garin Yankin ya bada sanarwa.Bayanai na nuna cewa gidaje samada 20,000 suka lalace sakamakon girgizan kasar.