Ethiopia

Kungiyar Kasashen Afrika Na Son Kawo Karshen Yaki A Libya

Shugaban Hukumar Tarayyar Africa Jean Ping
Shugaban Hukumar Tarayyar Africa Jean Ping RFI

Shugabannin kasashen Afrika yau sun nemi a kawo karshen yakin da akeyi a kasar Libya domin samun warware rikicin ta hanyar lumana. Shugabannin na Magana ne a taron su na musamman da sukayi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, gameda kasar Libya.Kwamashinan kungiyar Kasashen Afrika  mai kula da zaman lafiya da tsaro Ramtane Lamamra ya fadi cewa 'a tsaida hare- haren da Kungiyar NATO ke ta kaiwa kasar Libya domin daukan matakin siyasa a warware takaddamar.'Saidai kuma wakilin ‘yan tawayen kasar ta Libya dake halartan taron Abdalla Alzubedi ya tsaya kai da fata cewa hare-haren da ake kaiwa Dakarun Shugaba Moammar Gaddafi zai hana su kashe fararen hula dake kasar.Yace ba don Dakarun NATO na aikin su ba da kuwa Dakarun Moammar Gaddafi sunyi kisan kiyashi a kasar.