Faransa

An kalubalanci Faransa game da saka Hijabi dake rufe fuska

Reuters/Farid Alouache

Wani bawan Allah da matarsa dukkanin su musulmi ‘yan kasar Faransa dake zaune a Birtaniya sun kalubalanci hana matarsa saka hijabi, a fadin kasar Faransa.Miji da matar, sun shigar da kara ne gaban Kotun kare hakkin dan Adam ta Turai inda suke kalubalantar Gwamnatin kasar Faransa saboda hana musulmi mata sanya hijabin.Bayanin karar na cewa matakin Gwamnatin kasar Faransa ya takaita masu zirga-zirga akasashen Turai, inda ita maccen ke neman a biya ta Fam na Amirka dubu 10 saboda taba harkan rayuwar ta.A watan shekaranjiya ne dai kasar Faransa ta kasance kasa ta farko a Turai data hana mata sanya hijabi mai rufe dukkan fuska