Somaliya

An bindige Dan majalisar Somaliya

Reuters/Reisal Omar

Rahotanni Daga kasar Somaliya, sun ce wasu 'yan bindiga sun harbe wani Dan Majalisa har lahira, a Mogadishu babban birnin kasar.Wani shaidan gani da ido, Kalif Jire Warfa, ya ce an harbe Dan Majaliosar ne da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya Lahadi.Dakarun kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Kasashen Tarayyar AFrika, na aikin neman tabbatar da zaman lafiya cikin kasar ta Somaliya, wadda ta shafe shekaru 20 ana tashin hankali, abun da ya zama ruwan dare gama duniya.