Libya

Faransa ta baiwa 'yan tawayen Libya dala milyan 259 na kasar data rufe

© RFI

Kasar Faransa ta baiwa ‘Yan tawayen kasar Libya kudaden shugaban kasar Mu’ammar Ghadafi da a baya ta rike.Kudaden dai sun kai EURO Miliyon 181, kimanin Dalar Amurka miliyon 259.Sabon jakadan ‘yan tawayen a kasar Faransa, Mansur Seif al-Nasr da ke jawabi bayan tattaunawa da ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe, ya ce dama kudaden na jama’ar kasar Libya ne, kuma za ayi amfani da su ne wajen sayen abinci da magunguna ga jama’ar.