Faransa

Faransa zata tallafa wa kasashen Gabashin Afrika

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy Reuters/E.Vidal

Kasar Fararansa tana shirin ninkawa har sau uku, kan tallafin da take bayarwa a yankin kahon Africa da ke fama da yunwa.Shugaba Nicolas Sarkozy, wanda ya bayar da wannan sanarwar ya ce yanzu Faransa za ta bayar da tallafin Euro miliyo 30, ya kuma yi tayin bayar da tallafin kayan aikin da za ayi amfani da su waje rabon kayan agaji.MDD ta ayyana cewa ana fama da annobar yunwa a yankuna biyu na kudancin kasar Somaliya, kuma matsalar fari ta fi yin illa ga jama’ar kasar da yaki ya daidaita.