AU

Kungiyar Tarayyar Afrika zata tallafa game da fari

REUTERS/Feisal Omar

Kungiyar Kasashen Tarayyar Afrika, ta AU, ta ce zata gudanar da wani taron bada agaji, dan tallafawa Yankuna dake fama da tsananin fari a nahiyar.Mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar, Erastus Mwencha, ya ce ya zama wajibi kowacce kasa ta bada nata gudumawar, ganin yadda mutane ke rasa rayukansu kan wannan bala’i.Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar Dala biliyan biyu da rabi, wajen samarwa mutanen dake yankin Gabashin Africa abinci.