MEXICO

Mahukuntan Mexico sun Cafke wani shugaban masu ma'amalla da miyagun kwayoyi

©Reuters.

Yan Sanda a kasar Mexico, sun ce wani mai hada hada da miyagun kwayoyi da suka yi nasarar kamawa, Jose Antonio Acosta Hernandez, ya amsa laifin hanu wajen kashe mutane 1,500.Bayan sun nuna cewar, Hernandez, na da hannu wajen kashe wata ma’aikaciyar ofishin Jakadancin Amurka da mijinta, a garin Ciudad Juarez, wanda yayi kaurin suna wajen tashe tahen hankula, in da aka kashe mutane sama da 3,000 bara.