Masar

Tsohon Shugaban Masar Mubarak zai fuskanci Kotu

Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak Reuters/Amr Abdallah Dalsh

Mahukuntan kasar Masar sun saka jibi Laraba uku ga wannan wata na Agusta, domin fara shariyar tsohon Shugaban kasar Hosni Mubrak.Kamfanin Dillancin Laraban kasar ya ruwaito cewa shariyar ta ranar Laraba za a nuna kai tsaye ta tashoshin talabijin.Mubarak zai fuskancin shariyar tare da ‘ya’yansa maza biyu Gamal, wanda kafin faruwar haka ake ganin zai gaji kujerar shugabancin kasar da kuma Alaa, sai kuma tsawon Ministan Harkokin Cikin Gida Habib al-Adli, da wasu jami’an ‘yan sanda shida. Ana cajin mutanen da lafuku daban daban kama daga almunhanan kudade, da kuma kisan masu zanga zanga.Wata majiya ta kusa da tsohon Shugaba Murabak, ta bayyana cewa ba zai iya fuskantar shariyar ba, saboda dalilan rashin lafiya, bayan kwantar da shi, a asibitin garin Sharm el-Sheikh.Juyin juya harin watan Febrairu ya yi gaba da gwamtain Mubarak ta shekaru 30, kuma yanzu masu zanga zangar na ganin tamkar mahukuntan mulkin sojan kasar ta Masar, na amfani da rashin lafiya, domin tsohon Shugaba ya kaucewa amsa tambayoyi, laifukan da suke zarginsa da aikatawa.