Turkiya

Turkiya na Shirin Nada sabbin Habsoshin Soja

PM Turkiya Tayyip Erdogan
PM Turkiya Tayyip Erdogan

Gwamnatin kasar Turkiya ta fara nada manyan habsoshin sojan kasar.Wannan shi ne karon farko da gwamnatin farar hula ta nada shugabannin rindinonin sojan kasar ta Turkiya. Haka ya biyo bayan murabus da manyan habsoshin sojan kasra suka yi.Jami’an sun yi murabus domin nuna rashin jin dadi kan yadda aka cafke wasu sojoji da ake zargin suna yunkurin kifar da gwamnatin kasar.PM Tayyip Erdogan ke jagorancin majalisar soja ta kasar.