Amurka

Yan siyasan Amurka sun cimma yarjejeniyar karbar bashi

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya sanar da cimma wata yarjejeniya tsakanin 'yan Majalisun Jam’iyar Democrat da Republican, dangane da kara yawan adadin bashin da kasar zata iya ci.Shugaban ya sanar da zabtare kashe Dala Tiriliyon daya, a cikin shekaru 10, da kuma kafa kwamiti dan zai bada shawara kan yadda za’a dada rage gibin kasafin kudi.Tuni Shugaban Hukumar Bada lamini ta Duniya, IMF, Christine Lagarde, ta yaba da yarjejeniyar da aka cimma, wajen magance rikicin bashin kasar Amurka.Yayin da take jawabi, Largarde ta ce, rage darajar kudin Amurka, ba wai zai shafi kasar bane, har ma da tattalin arzikin duniya baki daya.