Libya

An yi bata kashin tsakanin dakarun Libya da Yan Tawaye

REUTERS/Thaier al-Sudani

Yan tawayen kasar Libya sun kara da dakarun dake biyayya wa Shugaba Muammar Gaddafi, na tsawon sa’oi cikin yankin gabashin kasar.Wani kakakin ‘yan tawayen ya bayyana cewa fadan ya barke, yayin da dakarunsu suka farma wasu tsageru masu dauke da makamai, wadanda ke tallafa wa dakarun Gaddafi.Akalla ‘yan tawaye shida sun rasa ransu, yayin bata kashin da bindigogi masu sarrafa kansu.A wani labarin gwamnatin kasar Jamus, ta ce bayan tattaunawa da kafofin tsaron kasar, ta sallami babban jami’in diplomasiyar Libya, Hisham al-Sharif, saboda ci gaba da goyon bayan Shugaba Gaddafi. Ta bukaci ya tattara da iyalansa.