Malawi

Dan uwan Shugaba Bingu wa Mutharika na Malawi zai yi Takara

Shugaban kasar Malawi Bingu  wa Mutharika.
Shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika. Reuters / Irada Humbatova

Jam'iyya Shugaba Bingu wa Mutharika, na kasar Malawi, ta zabi kaninsa a matsayin Dan takaran shugabancin kasar, a zaben shekarar 2014.Gidan Radion kasar, ya sanar da cewar, an zabi Peter wa Mutharika, farfesan shari’a, kuma Ministan ilimi a matsayin wanda ake saran zai maye gurbin shugaba mai ci.